Red Cross:Yunwa Zata Kashe Dubban Mutanen A Yankin Tigray Na Kasar Habasha

2021-02-11 15:00:38
Red Cross:Yunwa Zata Kashe Dubban Mutanen A Yankin Tigray Na Kasar Habasha

Kungiyar bada agaji ta Red Cross ta kasar Habasha ta bada sanarwan cewa, mai yuwa dubban mutane su rasa rayukansu a yankin Tigray na arewacin kasar sabuda yunwa. Kungiyar ta ce a halin yanzu kashi 80% na mutanen yankin suna fuskantar karancin abinci.

Tashar talabijin ta Prestv a nan Tehran ta nakalto Abera Tola, shugaban kungiyar bada agaji ta Red Cross na kasar Habasha ta na fadar haka a jiya Laraba a wani taron ‘yan jarida da ta kira.

Tola ta kara da cewa har yanzun ana ci gaba da fafatawa tsakanin yan tawaye da kuma sojojin gwamnatin kasar ta Habasha a lardin, wanda ya hana jami’an agaji isa wurare da dama a Lardin.

Tola ta kara da cewa, ya zuwa yanzu dai sun sami labarin cewa mutane da dama a birnin Mekelle babban birnin Lardin da kuma wasu wurare kewaye da shi sun fara shiga mummunan hali na rashin abinci.

Idan an dade ba’a bada damar isar jami’an kungiyar zuwa wadannan yankuna da sauri ba, mai yuwa dubban mutane za su rasa rayukansu saboda karancin abinci. Daga karshe kungiyar ta bayyana cewa kimanin mutane miliyon 6 ne suke bukatar abinci a yankin na Tigray a halin yanzu.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!