2021 FIBA:’Yan Wasa 6 Sun Karbi Gayyata Daga Kungiyar Wasan Kwallon Kwando Na Najeriya D’Tigers’

2021-02-11 14:50:20
2021 FIBA:’Yan Wasa 6 Sun Karbi Gayyata Daga Kungiyar Wasan Kwallon Kwando Na Najeriya D’Tigers’

Hukumar wasan kwallon Kwando ta tarayyar Najeriya wato ‘Nigerian Basket Balla Federation’ ko (NBBF) ta bada sanarwan cewa ta aikewa ‘yan wasan kasar guda 6 wadanda suke yin wasannin a kasar Faransa, gayyata zuwa shirye-shiryen gasar FIBA 2021 wacce za’a gudanar a kasar Tunisia.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta kara da cewa hukumar NBBF ta fitar da sunayen ‘yan wasa 12 a ranar litinin da ta gabata, wadanda zasu yiwa kungiyar wasan kwallon Kwando ta kasar D’Tigers wasa. 6 daga cikinsu suna gudanar da wasannin a halin aynzu a kasar Faransa.

Labarin ya kara da cewa a halin yanzu Najeriya ce a sama a group B bayan da ta lallasa kasashen Ruwanda, Mali da kuma Sudan ta Kudu. Sannan ana saran kungiyar ta D’Tigers za ta kai ga samun nasara tare da wadannan yan wasan da aka gayyata daga kasashen Faransa da kuma Turkiyya.

Banda haka hukumar ta NBBF ta ce akwai wasu ‘yan wasan da suke jira, idan ana bukatarsu zasu iya shiga gasar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!