Kungiyar Hamas Ta Palasdinu Ta Gode Wa Iran Saboda Taimakon Da Take Bai Wa Al’ummar Palasdinu

2021-02-11 08:48:28
 Kungiyar Hamas Ta Palasdinu Ta Gode Wa Iran Saboda Taimakon Da Take Bai Wa Al’ummar Palasdinu

Shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas, Isma’ila Haniyyah wanda ya aikowa da jagoran juyin musulunci na Iran wasika akan zagayowar lokacin cin nasarar juyin musulunci, ya bayyana cewa: “ Muna yi muku godiya akan taimaka wa al’ummar Palasdinu da kuma gwgawarmayarta.”

Haniyyah ya ci gaba da cewa; “Kungiyar Hamas, da kuma al’ummar Palasdinu muna taya ku murna akan zagayowar lokacin cin nasarar juyin musulunci, sannan kuma muna yi mu ku godiya akan matakai na mutunci da kuke dauka da kuma take ci gaba akan Palasdinu da taimakon gwgawarmaya.”

Har ila yau shugaban na kungiyar Hamas ya bayyana fatansa na ganin cewa alaka jamhuriyar musulunci ta Iran ta ci gaba da tafiya akan tafarkinta na taimakawa al’ummar Palasdinu.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!