Iran Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai A Birnin Kabul Na Afghanistan

2021-02-11 08:41:44
Iran Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai A Birnin Kabul Na Afghanistan

Iran Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai A Birnin Kabul Na Afghanistan

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya yi tir da harin da aka kai a jiya Laraba a birnin Kabul tare da yin kira ga dukkanin wadanda su ka damu da makomar Afghanistan, da su yi tare domin kawo karshen tashe-tashen hankula a fadin kasar.

A jiya Laraba ne dai aka kai hari a birnin Kabul wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkata mutane da dama.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran din ya kuma kira yi masu fada a kasar ta Afghanistan da su takawa masu zubar da jini birki.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!