Yadda Ranar Cikar Shekaru 42 Na Juyin Juya Halin Muslunci A Iran Ta Dauki Hankula A Duniya

A yau ne ake gudanar da bukukuwan
cikar shekaru 42 da samun nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran.
Kafofin yada labarai da dama na
duniya sun mayar da hankali a kan yadda a yau juyin juya halin muslunci na
kasar Iran ke cika shekaru 42, bayan kifar da gwamnatin kama karya ta sarki
Shah, karkashin jagorancin marigayi Imam Khomeni.
Daga kafofin yada labarai na yankin
gabas ta tsakiya da suka mayar da hankali kan wannan rana akwai tashar
Aljazeera, wadda tun a safiyar yau wakilanta suke gudanar da ayyukan daukar
rahotanni a cikin birnin Tehran da kewaye.
Baya ga haka kuma wasu daga cikin
kafofin yada labaran yankin, tashar Almayadeen daya daga cikin fitattun
tashoshin larabawa da ke watsa shirinta daga kasar Lebanaon, a yau ta mayar da
labarin cikar shekaru 42 da samun nasarar juyin juya halin muslunci a Iran ya
zama daga cikin muhimman labaranta.
Baya ga tashoshin larabawa da sauran
kafofin yada labarai na yankin gabas ta tsakiya, wasu daga cikin muhimman
kafofin yada labarai na duniya, da suka hada da kamfanin dillancin labaran
Associated Pres, da kuma Reuters, gami da Agency of France Press, duk sun dauki
wannan labari.
Haka nan kuma manyan tashohi da
kamfanonin dllancin labarai na kasashen Rasha, da suka hada da tashar RT, gami
da kamfanin dillancin labarai na sputnik da iterfax da sauransu, duk sun dauki
wannan labari a cikin manyan labaransu na yau.
015