Gwamnatin Jamhuriyar Nijar Ta Yi Maraba Da Kaddamar Da Shirin Shimfida Layin Dogon Da Zai Hada Kasar Da Jamhyuriyar Nijar

2021-02-10 11:50:43
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar Ta Yi Maraba Da Kaddamar Da Shirin Shimfida Layin Dogon Da Zai Hada Kasar Da Jamhyuriyar Nijar

Pira ministan jamhuriyar Nijar, Brigi Rafini da sauran jami’an gwamnati ya bibiyi yadda shugaban kasar Nigeria Muhammadu Buhari ya kaddamar da shimfida layin dogo da zai hada kasashen biyu, ta hanyar bidiyo.

A jiya Talata ne dai shugaban kasar Nigeria Muhammadu Buhari ya kaddamar da shimfida layin jirgin kasa wanda zai tashi daga kano zuwa Maradin Jamhuriyar Nijar.

Layin jirgin kasan mai nisan kilo mita 240 zai ci kudin da su ka kai dalar Amurka biliyan 1.96, kuma wani kamfani ne na kasar Portugal zai yi aikin.

Wadanda su ka gabatar da jawabai a wurin bikin, sun bayyana cewa; Idan aka kammala hanyar jirgin kasan, za ta taimaka matuka wajen bunkasa harkokin zirga-zirga da kuma kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!