Najeriya: Masu Dauke Da Makamai Sun Kashe Mutane 23 A Jihar Kaduna
2021-02-10 11:47:04

Masu Dauke Da Makamai Sun Kashe Mutane 23 A Jihar Kaduna
Rahotannin da suke fitowa daga jihar Kaduna sun
ce masu dauke da makamai sun kai hare-hare a kananan hukumomi biyar da suka
hada, Birnin-Gwari, Giwa, Chikun, Igabi da Kauru.
Kwamishinan harkokin tsaron da cikin gida Mr. Samuel Aruwan, ya fada a jita Talata cewa A Birnin Gwari maharan sun kashe mutane 10, tare da ambaton sunayensu.
A can Igabi
kuwa, maharan sun kashe wani mutum guda sai kuma a karamar hukumar Giwa inda
can ma su ka kashe wani mutum daya.
Jumillar
mutanen da aka kashe sun kai 23.
Jihar Kaduna
dai tana cikin jihohin da suke fama da hare-haren masu dauke da makamai da kuma
yin garkuwa da mutane.
031
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!