An Fara Gudanar Da Jerin Gwanon Tunawa Da Ranar Cin Nasarar Juyin Musulunci A Iran

2021-02-10 11:33:22
 An Fara Gudanar Da Jerin Gwanon Tunawa Da Ranar Cin Nasarar Juyin Musulunci A Iran

An Fara Gudanar Da Jerin Gwanon Babrura Na Tunawa Da Ranar Cin Nasarar Juyin Musulunci A Iran

Da safiyar yau Laraba ne mahaya babura da motoci su ka yi jerin gwano domin munar zagayowar ranar da juyin musulunci a Iran ya kai ga cin nasara shekaru 42 da su ka wuce.

Ana yin jerin gwanon nan a ciki birane da garuruwa daban-daban na Iran cikin kula da matakan hana yaduwar cutar corona.

A shekarar 1979 ne yunkurin juyin musulunci a karkashin jagorancin marigayi Imam Khumain ya kai ga samun nasarar kifar da gwamnatin tsarin sarauta da shekaru 2500.

A tsawon daron jiya al’ummar Iran din sun rika bayar da kabarbari a saman gidajensu wanda yake tunawa da yadda ta kasance a ranar karshe ta mulkin tsarin sarauta.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!