Iran:Alkalin Alkalan Kasar Iran Ya Gana Da Firai Ministan Kasar Iraki Mustafa Alkazimi

2021-02-10 08:53:07
Iran:Alkalin Alkalan Kasar Iran Ya Gana Da Firai Ministan Kasar Iraki Mustafa Alkazimi

Alkalin alkalan kasar Iran Hujjatul Islami Ibrahim Ra’isi wanda yake ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Iraqi, a jiya da yamma ya gana da firai ministan kasar ta Iraki Mustafa Al-Kazimi.

Majiyar muryar Jumhuriyar Mususlunci ta Iran ta bayyana cewa a ganawar bangarorin biyu an tattauna hanyoyin aiki tare don ci gaban kasashen biyu.

Har’ila yau an shirya ganawar Sayyeed Ibrahim Ra’isi da shugaban kasar Iraki Barham Saleh da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Muhammad Halbusi kafin Sayyid Ra’isi ya dawo gida.

Sayyeed Ra’isi ya isa kasar Iraqi ne a ranar Litinin tare da gayyatar alkalin alkalan kasar ta Iraki Fa’iq Zaidan.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!