Falasdinu: Kungiyar ‘Jihadul Islami' Ta Ce Ba Zata Shiga Cikin Zabubbukan Kasar Ba

2021-02-10 08:40:24
Falasdinu: Kungiyar ‘Jihadul Islami' Ta Ce Ba Zata Shiga Cikin Zabubbukan Kasar Ba

Kungiyar ‘Jihadul Islami’ daya daga cikin manya-manyan kungiyoyi masu gwagwarmaya da Isra’ila saboda mamayar da yahudawan Isra’ila suka yiwa kasarsu, ta bayyana cewa ba zata shiga zabubbukan kasar wadanda za’a gudanar nan gaba a cikin wannan shekarar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto kungiyar ta na fadar haka a jiya Talata a taron kungiyoyin Falasdinawa a birnin Alkahira na kasar Masar.

Jihadul Islami ta kuma kara da cewa ta dauki wannan matakin ne don ta fahinci cewa za’a gudanar da zabubbukan ne bisa tsarin ‘yarjejeniyar Oslo’tsakanin Falasdinaw ada yahudawa ta shekara 1993-1995, wacce a wajenta ba zai kai Falasdinawa ga samun cikekken ‘yancinsu daga hannun Isra’ila ba.

Kafin haka dai a ranar litinin da ta gabata ce kungiyoyin Falasdinawa 15 suka fara taro a birnin Alkahira na kasar Masar don dinke barakan da ke tsakaninsu da kuma tattauna yadda za su gudanar da zabubbuka na majalisar dokoki da kuma shugaban kasa a yankunan yamma da kogin Jordan, birnin Qudus da kuma zirin Gaza.

Za’a gudanar da zaben majalisar dokokin Falasdinawan ne a ranar 22 ga watan Mayu na wannan shekara sannan a gudanar da na shugaban kasa kuma a ranar 31 ga watan Yulin shekara ta 2021 da muke ciki.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!