Iran Ta Kaddamar Da Yi Wa Jama’arta Riga Kafin Korona
2021-02-09 21:32:28

A Iran, yau Talata, aka fara yi wa jama’a riga kafin cutar korona, kamar yadda shugaban kasra ya bukata.
Dan ministan kiwon lafiya na kasar ne mutum na farko da aka fara yi wa allurar riga kafin, samfarin Sputnik V, ta kasar Rasha.
Ministan kiwon lafiya na Iran, Saeed Namaki, ya bayyana fara yin riga kafin cutar daga iyalensa domin kwantar wa da jama’ar kasar hankali game da sahihancin maganin.
A ranar 4 ga watan nan ne Iran, ta karbi kashin farko na alluran riga kafin daga kasar Rasha.
An kaddamar da yin alluran ne a cikin asibitoci 625 na kasar, inda
za’a fara wa ma’aikatan lafiya, sai kuma masu yawan shekaru da masu jinya, inda
ake fatan yi wa kashi 70 cikin dari na jama’ar kasar riga kafin.
024
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!