Amurka : An Fara Shari'ar Tsige Trump A Karo Na Biyu

2021-02-09 21:24:52
Amurka : An Fara Shari'ar Tsige Trump A Karo Na Biyu

A Amurka yau Talata, aka fara sauraron karar sake tsige tsohon shugaban kasar Donald Trump a majalisar dattawa.

Za a fara Shari’ar mai cike da tarihi, ta tsige tsohon shugaban kasar, karo na biyu, inda ake zargi Trump da ingiza magoya bayansa, tayar da bore a majalisar dokokin kasar yau kusan wata guda da ya wuce.

Zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali, yayin da magoya bayan Trump suka afkawa ginin Majalisar, da nufin hana tabbatar da nasarar dan takarar jam’iyyar demokrate Joe Biden a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar na 2020.

Mutane biyar ne suka mutu, ciki har da wani jami'in 'yan sanda yayin tarzomar a ginin majalisar na capitol Hill a ranar 6 ga watan Janairu da ya gabata.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!