Iran : Hukuncin Belgium, Ya Sabawa Yarjejeniyar Diflomasiyya

2021-02-09 21:22:36
Iran : Hukuncin Belgium, Ya Sabawa Yarjejeniyar Diflomasiyya

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, ta yi allawadai da hukuncin zama gidan yari na tsawon shekaru 20 da wata kotun Belgium ta yake kan wani jami’in diflomasiyyan ta.

Wannan a cewar ma’aikatar harkokin waken kasar ta Iran, ya nuna yadda kasashen turai suka zama ‘yan amshin shatan kungiyar ‘yan ta’adda ta Moudjahidines-e-Khalq (KMO).

A ranar Alhamis data gabata ne wata kotun Belgium, ta yanke hukunci kan jami’in diflomatsiyyan na Iran, mai suna Assadollah Assadi, bisa zarginsa da hannu a kisa wani hari kan taron ‘yan kungiyar ta MKO a birnin Paris, a cikin shekarar 2018.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh, duk tuhume tuhumen da ake wa jami’in basu da tushe, kuma sun sabawa yarjejeniyar kasa da kasa da kuma yarjejeniyar Vienna ta 1961, wacce ta tanadi huldar diflomatsiyya, don haka Iran, ke mai watsi da dukkan hukunce hukuncen kotun.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!