Masar Ta Bude Kan Iyakarta Da Zirin Gaza Na Falasdinu

2021-02-09 21:19:43
Masar Ta Bude Kan Iyakarta Da Zirin Gaza Na Falasdinu

Kasar Masar ta sanar a wannan Talata, da bude iyakarta da zirin Gaza, har na tsawon wani lokaci da ba’a kayyade ba.

Bude iyakar shi ne irinsa na farko a cikin tsawon shekaru, kamar yadda wani jami’in tsaron kasar ta Masar, ya sanar.

Haka kuma bude iyakar na zuwa ne bayan bude wata tattaunawa jiya Litinia birnin Alkahira, tsakanin kungiyoyin hammaya na Falasdinu, ciki har da Fatah

da kuma Hamas da zumar shirya zabe wadan shi ne irinsa na farko a cikin shekaru 15.

Tattaunawar za ta shafi muhimman batutuwa da suka hada da yin sulhu a tsakaninsu da kuma yadda za a gudanar da muhimman zabuka.

Yau Talata ne ake sa ran kawo karshen tattaunawar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!