Ra’isy: Za A Dauki Fansar Shahadar Sulaimani Abu Mahadi Muhandis

2021-02-09 09:03:42
  Ra’isy:  Za A Dauki Fansar Shahadar Sulaimani  Abu Mahadi Muhandis

Babban alkalin alkalan Iran, Ibrahim Ra’isy wanda ya isa birnin Bagadaza domin ziyarar aiki ne bayyana cewa; Tabbas za a dauki fansar kisan da Amurka ta yi wa Kassim Sulaimani da Abu Mahdi al-Muhandis.

Ra’isy ya ziyarci wurin da kwamandojin biyu su ka yi shahada a kusa da filin saukar jiragen sama na Bagadaza, inda ya bayyana yadda Amurka ta yi furuci da kirkirar kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Shugaban ma’aikatar shari’ar ta Iran ya kuma kara da cewa; Shahidan biyu suna a matsayin manyan alami ne na daukaka da karfin da al’ummar musulmi su ke da su, kuma za su ci gaba da zama a matsayin hakan har abada.

Ra’isy ya kuma jinjinawa al’ummar Iraki, inda ya bayyana cewa; suna tafiya ne akan tafarki daya na gwgawarmaya.

Ziyarar da Ibrahim Ra’isy tana a matsayin amsa kira ne na shugaban hukumar shari’a ta kasar Iraki.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!