Kungiyoyin Palasdinawa Sun Bude Tattaunawa Akan Muhimman Batutuwa A Jiya Litinin A Kasar Masar

2021-02-09 09:00:56
 Kungiyoyin Palasdinawa Sun Bude Tattaunawa Akan Muhimman Batutuwa A Jiya Litinin A Kasar Masar

Tattaunawar da aka fara a birnin al-kahira za ta shafi muhimman batutuwa da suka hada da yin sulhu a tsakaninsu da kuma yadda za a gudanar da muhimman zabuka.

Muhimman kungiyoyin Palasdinawa da su ka kunshi Hamas, Jihadul-Islami, PLO da dukkanin kungiyoyin da su ka rattaba hannu akan yarjejeniyar 2011 suna daga cikin masu halartar taron.

Shugaban kungiyar Hamas, Isma’ila Haniyyah ya gabatar da jawabi da a ciki ya bayyana cewa; tattaunawar tana da matukar muhimmanci, kuma ci gaba ne da tattaunawar da aka bude a baya.

Har ila yau Isma’ila Haniyyah ya ce; Muna sane da yanayi mai hatsari da muke ciki a yanzu na batutuwan birnin kudus, da hakkin komawa gida, don haka muna da nauyin da ya rataya a wuyanmu baki daya.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!