​Zarif: Iran Tana Goyon Bayan Majalisar Dinkin Duniya Domin Kawo Karshen Yaki A Yemen

2021-02-08 20:14:19
​Zarif: Iran Tana Goyon Bayan Majalisar Dinkin Duniya Domin Kawo Karshen Yaki A Yemen

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad zarif ya bayyana cewa, kasar Iran tana goyon bayan duk wani yunkuri da zai taiamaka wajen kawo karshen yaki a kan al’ummar kasar Yemen.

A lokacin da yake zantawa yau tare da manozon musamman na majlaisar dinkin duniya kan rikicin Yemen Martin Griffihts a birnin Tehran, Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad zarif ya bayyana cewa, kasarsa tana mara baya ga duk wani yunkuri na Majalisar Dinkin Duniya, da sauran bangarori na duniya, da zai taiamaka wajen kawo karshen yaki a kan al’ummar kasar Yemen.

Ya ce daukar matakin dakatar da yakin shi ne abu mafi muhimmanci a matakin farko, sannan batun taimaka ma al’ummar kasar da aka daidaita musu kasa bayan kisan kiyashin da aka yi musu, sannan kuma a warware sauran matsaloli ta hanyoyin na siyasa da diflomasiyya.

A nasa bangaren manozon musamman na majlaisar dinkin duniya kan rikicin Yemen Martin Griffihts ya bayyana cewa, mahangar Iran da majlaisar dinkin duniya kan yadda ya kamata a warware rikicin Yemen ta yi kama, domin kuwa dole ne a dakatar da yaki, sannan a samu damar gudanar da ayyuka na jin kai, tare da mayar da dukkanin bangarorin siyasar kasar kan teburin tattaunawa.

A bisa rahotanni da majalisar dinkin duniya gami da kungiyoyin farar hula masu zaman kansu a duniya suka bayar, a cikin shekaru 6 da Saudiyya ta kwashe tana kaddamar ad yaki kan al’ummar kasar Yemen, fiye da fararen hula dubu 17 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren, yayin da kuma wasu dubban sun mutu sakamakon killace kasar da kuma jefa rayuwarsu cikin matsanancin hali, na rashin abinci da magunguna, da ma haramta musu mafi karancin abin da suke bukata domin rayuwa.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!