Sudan: A Yau Ne Ake Sa Ran Fitar Da Bayani Kan Kafa Sabuwar Majalisar Ministoci

Firayi ministan gwamnatin rikon
kwarya a kasar Sudan Abdullah Hamduk ya sanar da cewa, a yau ne ake sa ran
fitar da bayani kan yadda za a kafa sabuwar gwamnati a kasar.
Tashar Almayadeen ta bayar da
rahoton cewa, bisa bayanan da ofishin firayi ministan kasar Sudan Abdullah
Hamduk ya fitar, a yau ne ake sa ran dukkanin bangarori za su kammala mika
sunayen ‘yan takararsu domin rike mukamai a majalisar ministocin kasar.
Wannan mataki dai yana zuwa ne bayan
rusa majalisar ministocin da firayi ministan na Sudan ya yi a jiya Lahadi, inda
ya sanar da cewa dukkanin bangarorin siyasa da ya kamata su mika sunayen ‘yan
takarar neman kujerun ministoci, a yau Litinin ne za su kammala mika sunayen
nasu.
Firayi ministan gwamnatin rikon
kwarya a kasar ta Sudan Abdullah Hamduk ya rusa gwamnatin ne biyo bayan
barazanar da shugaban majalisar shugabancin kasar Abdulfattah Burhan ya yi ne,
inda ya bayyana cewa idan bangarorin siyasa ba su mika sunayen ‘yan takararsu
ba, to zai rusa majalisar ministoci.
Tun bayan faduwar gwamnatin tsohon shugaban kasar ta Sudan Umar Hassan Albashira cikin watan Agustan shekara ta 2019, kasar take fuskantar matsaloli na tatalin arziki, duk kuwa da alkawullan da kasashen turai da na larabawa suka wa kasar, na habbaka tattalin arzkinta.
015