​Qalibaf Ya Mika Sakon Jagoran Juyin Juya Halin Muslunci Zuwa Ga Shugaba Putin Na Rasha

2021-02-08 17:51:15
​Qalibaf Ya Mika Sakon Jagoran Juyin Juya Halin Muslunci Zuwa Ga Shugaba Putin Na Rasha

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Baqir Qalibaf, ya mika wa takwaransa na Rasha sakon jagoran juyin juya halin muslunci zuwa ga shugaba Putin.

Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, a yau shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Baqir Qalibaf, ya mika wa shugaban majalisar dokokin kasar Rasha Vyacheslav Volodin sakon jagoran juyin juya halin muslunci Ayatollah Sayyid Ali Khamenei,zuwa ga shugaba Vladimir Putin na kasar ta Rasha a birnin Moscow.

Tun a yammacin jiya ne shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya isa birnin Moscow dauke da sakon na jagora, inda a ziyarar tasa zai gana da manyan jami’ai daban-daban na gwamnatin kasar Rasha.

Bayan isarsa birnin Moscow, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa, alaka tsakanin Iran da Rasha tana nan daram, kuma za ta ci gaba da kara bunkasa a dukkanin bangarori, kamar yadda kuma sauye-sauye a siyasar duniya ba za su taba yin tasiri a kan kawancen da ke tsakanin Rasha da Iran ba.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!