​Netanyahu Ya Gurfana A Gaban Kotu Bisa Tuhumar Cin Hanci Da Karbar Rashawa

2021-02-08 17:26:45
​Netanyahu Ya Gurfana A Gaban Kotu Bisa Tuhumar Cin Hanci Da Karbar Rashawa

Firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana yau a gaban kotun Isra’ila a birnin Quds, bisa tuhumce-tuhumce na cin hanci da rashawa da ke kansa.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayar da rahoton cewa, a yau firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya gurfana a gaban kotu a birnin Quds, kan zarge-zargen da suke a kansa da suke da alaka da cin hanci da kuma karbawar rashawa.

Netanyahu dan shekaru 71 da haihuwa, wanda ya kwashe tsawon shekaru 12 a jere yana rike da kujerar firayi ministan Isra’ila tun daga shekara ta 2009, ya musunta dukkanin tuhumce-tuhumcen da aka gabatar masa a gaban kotu.

Ya kwashe tsawon mintuna 20 yana magana tare da karyata dukkanin zargin da ake yi masa, na karbar rashawa daga manyan kamfanoni, da kuma yin amfani da matsayin wajen arzurta kansa ta wasu hanyoyi.

A zama na gaba dai kotun za ta saurari shedu ne kan wadannan tuhumce-tuhumce a kan Benjamin Netanyahu, kamar yadda kuma kotu taki amincewa da bukatar da lauyoyinsa suka gabatar, na neman a daga shari’ar domin ba su wadataccen lokaci.

Babban lauyan da ke jagorantar tawagar lauyoyi masu kare Netanyahu ya bayyana cewa, aike wa Netanyu sammaci da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya, babban cin zarafi ne a gare shi da kuma mukamin da yake rike da shi, yayin da babban mai shigar da kara na Isra’ila ya bayyana hakan da cewa yana kan doka.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!