Iran: An Mika Wa Dakarun Kare Juyin Musulunci Kwale-kwalen Yaki 340 A Yau Litinin
2021-02-08 15:01:44

An Mika Wa Dakarun Kare Juyin Musulunci Na Iran Kwale-kwale Yaki 340 A Yau Litinin
Kamfanin dillancin labarun “Mehr”
ya ambato cewa; Da safiyar yau Litinin an gudanar da bikin mikawa dakarun
kare-juyin musulunci na Iran kwale-kwale da suke dauke da kayan yaki har 340, a
garin Bandar-Abbas.
Daga cikin mahalarta bikin da
akwai kwamandan dakarun kare-juyin musulunci na Iran Janar Husain Salami, da
kwamandan rundunar ruwa Admiral Ali Ridha Tankasir da kuma jami’an
tafiyar da sha’anin mulki a gunduar Hurzumgan.
Mika wa dakarun wadannan kwale-kwalen dai ya zo ne adaidai lokacin da ake bikin zagayowar ranakun cin nasarar juyin musulunci a Iran da aka yi a 1979.
031
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!