Tawag-tawaga Ta Kungiyoyin Palasdinawa Sun Fara Isa Kasar Masar Domin Bude Tattaunawa A Tsakaninsu

Tun da safiyar yau Litinin ne dai tawaga-tawaga ta kungiyoyin Palasdinawan ta fara isa birnin al-qahira domin yin tattaunawa ta kasa a tsakaninsu.
Majiyar Palasdinawa ta shaidawa
manema labaru cewa; tawagar kungiyar jihadul-Islami ta kunshi Muhammadul-Hindi
wanda shi ne jagoran bangaren siyasa na kungiyar, sai kuma Anwar Abu Taha da
Nafiz Azzam da Khalid Badhash, sai kuma Daud Shihab.
Ita kuma kungiyar Hamas ta aike
da tawagar da ta kunshi Yahya al-Sinwar, da Khalil Hayyah da Izzat al-Rashaq,
sai kuma HIsam Badran da Muhammad Nazal.
Dukkanin bangarorin
Palasdinawan sun bayyana yadda su ke son ganin an cimma matsaya guda akan
muhimman batutuwan da su ka shafi al’ummar ta Palasdinu.
A gobe Talata ne dai ake sa ran bude taron a tsakanin dukkanin bangarorin
Palasdinawa da su ka hada da gwamnatin kwarya-kwarya ta Palasdinawa.
.