Iran Ta Fitar Da Sabuwar Alluran Ragakafin Cutar Korona

2021-02-08 09:19:08
Iran Ta Fitar Da Sabuwar Alluran Ragakafin Cutar Korona

Za’a fara gwajin sabuwar alluran riga kafin cutar korona mai suna Razi Cov-Pars kan mutane a nan kasar Iran. Wannan shi ne alluran riga kafin cutar korona na biyu wanda ake yi a nan kasar Iran.

Tashar talabijin ta Presstv ta bayyana cewa a jiya Lahadi ce aka kaddamar da gwajin alluran Razi Cov-Pars kan jikin mutanen a nan birnin Tehran. Kafin haka dai an gwada alluran kan dabbobi kimani 500.

Labarin ya kara da cewa gwajin da za’a yi wa alluran a kan mutane dai ya na bukatar masu sa kai 133 wadanda za’a yi wa alluran har sau biyu. Bayan ta farkon da kwanaki 21 ne za’a yi masu na biyu.

Har’ila yau alluran tana da nau’inta na shaka wanda shi ma za’a fara gwada shi a kan mutane.

Bambancin wannan allluran da ta COVIRAN barakata dai shi ne an yi wannan alluran ne daga sinadarin Protien na jikin kwayar cutar ta Korona.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!