Najeriya: Gwamnan Kano Ya Amince A Gudanar Da Muhawara Tsakanin Malaman Kano Da Sheikh Abdul Jabbar
2021-02-08 09:09:08

Gwamnan jihar Kano Alhaji Dr Abdullahi Umar Ganduje ya amince a shirya muhawara tsakanin malaman jihar da kuma Sheikh Abduljabbar Nasiru nan da makonnin biyu don tantance wanda yake da gaskiya a tsakanin bangarorin biyu.
Kwamishinan addini na Jihar Dr Muhammad Taha Adamu ne ya bayyana haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa za’a watsa muhawarar tsakanin bangarorin biyu a kafafen yada labarai na ciki da wajen kasar kai tsaye.
Gwamnatin jihar Kano dai ta dakatar da sheikh Abbdur Jabbar Malam Nasiri daga gabatar da karatun da ya saba yi a masallacinsa a makon da ya gabata, saboda korafe-korafen da malaman kano suka kaiwa gwamnan kan cewa ya na bata magabata a karatunsa.
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!