Iran Ta Shaida Wa MDD, Cewa Ba Zata Lamunci Barazanar Isra’ila Ba

2021-02-07 22:02:30
Iran Ta Shaida Wa MDD, Cewa Ba Zata Lamunci Barazanar Isra’ila Ba

Iran, ta bayyana wa MDD, cewa ba za ta lamunci duk wata irin barazana ba daga Isra’ila.

A wata wasika da ya aike wa babban sakataren MDD, Antonio Guteress, wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Majid Takht-Ravantchi, ya ce koda wasa Iran, ba zata lamunci irin taken taken da Isra’ila ke yi mata ba, wanda ba zata yi wata-wata ba na maida kakkausan martani.

Iran ta ce duk wata barazana ko tsokana daga yahudawan sahayoniya, Iran ba za ta saurara ba, dan kuwa za ta maida martani fiye da yadda ake tunani.

M. Ravantchi, ya ce bayan kalamman data shafe dogon lokaci tana yi na tsokana da fitar bayanai marasa kan-gado kan Iran, yanzu Isra’ila ta fara mafarkin kai wa Iran hari.

Kan hakan ne wakilin Iran a MDD, ya ce, duniya ta kwana da sanin cewa duk ranar da Isra’ila ta yi gigin yunkuri ko kai mata hari, to kuwa Iran za ta maida kakkausan martani.

A kwanan baya ne dai kafofin yada labarai daga Isra’ila suka rawaito cewa, gwamnatin Netanyahu ta baiwa sojojin yahudawan umarnin tsara yadda za’a kai wa cibiyoyin nukiliyar Iran hari.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!