An Zabi Faki Mahamat, Domin Shugabancin (AU) A Wa’adi Na biyu

2021-02-07 21:57:24
An Zabi Faki Mahamat, Domin Shugabancin (AU) A Wa’adi Na biyu

Shugabannin kasashen Afrika sun sake zabar Moussa Faki Mahamat, domin ci gaba da shugabancin kwamitin gudanawar kungiyar tarayyar Afrika a karo na biyu na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Shugabannin kasashen Afrika sun sake zabarsa a lokacin taron kolin kungiyar karo na 34, wanda aka bude a jiya Asabar ta kafar bidiyo.

A cewar AU, mambobi 51 daga cikin 55 ne suka zabi Mahamat.

Dama dai Musa faki Mahamat, shi ne dan takara daya tilo da ya tsaya a zaben neman shugabancin kungiyar.

A ranar Asabar ne shugaban gudanarwar kungiyar ta AU ya gabatar da bayanan muhimman ayyukan da ya gudanar a wa’adin shugabancinsa na farko ga taron majalisar shugabannin kasashen Afrika.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!