Iran: Manzon MDD Kan Rikicin Kasar Yemen Ya Isa Birnin Tehran

2021-02-07 14:24:27
Iran: Manzon MDD Kan Rikicin Kasar Yemen Ya Isa Birnin Tehran

Jakadan MDD na musamman kan kasar Yemen ya isa nan birnin Tehran don tattauanawa da jami’an gwamnatin kasar kan lamuran da suka shafi yaki a kasar ta Yemen. Majiyar muryar JMI ta nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran tana cewa Martin Griffiths jakadan MDD na musamman kan yakin kasar Yemen ya isa birnin Tehran a safiyar yau Lahadi don ganawa da Jami’n gwamnatina kasar kan yakin kasar ta Yemen.

A cikin watan Maris na shekara ta 2015 ne gwamnatin kasar Saudiya tare da kawayenta na kasashen larabawa suka farwa kasar Yemen da yaki da nufin maida tsohon shugaban kasar Abdu Rabbu Mansur Hadi kan kujerar shugabancin kasar.

Yakin wanda kasashen Amurka da Turai suke goyon bayasa, a cikin shekaru 6 da suka gabata, sun sayarwa wadannan kasashen larabawa makamai masu yawa.

Har’ila yau MDD ta bayyana cewa fiye da rabin mutanen kasar suna rayuwa ne ta taimakon kungiyoyin bada agaji. An kashe mutane fiye da 100,000 sannan wasu da dama suka ji rauni a yayinda kasashen suka yiwa kasar kofar rago.

Sabuwar gwamnatin kasar Abuka dai ta ce zata matsawa kasashen laraba wa kawo karshen yakuin

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!