Amurka Na Shigar Da Kayayakin Yaki A Kasar Siriya

2021-02-07 14:20:09
Amurka Na Shigar Da Kayayakin Yaki A Kasar Siriya

Kafafen yada labarai na kasar Siriya sun bayyana cewa an ga motocin sojojin Amurka kimani 50 dauke da kayakin yaki da kuma makamashi zuwa cikin kasar Siriya daga kasar Iraki.

Tashar talabijin ta Rusiyal Yau ta kara da cewa motocin sun shiga kasar Siriya ne ta barauniyar kufar shiga kasar mai suna Al-Walid, inda suka nufi cikin kasar.

Labarin ya kara da cewa mai yuwa motocin zasu je Yankunan Dair- Zur da kuma Hasaka inda Amurka take da sansanonin sojojinta.

Kungiyar yan ta’adda ta kurdawan Kasad wacce take samun goyon bayan Amurka ce take taimkawa sojojin kasar na Amurka a irin wadannan ayyuka.

Kafin haka dai sojojin na Amurka wadanda suke mamaye da wasu yankuna a arewa maso gabacin kasar Siriya tun shekara ta 2016 suna satar danyen man fetur a yankin tare da taimakon kungiyar yan tawaye ta kurdawan kasar ta Siriya wacce ake kira Kasad.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!