Iran Ta Bukaci Kasashen Da Ke Yakar Yemen Su Janye Ma Ta Takunkumi
2021-02-07 09:16:18

Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen Iran Sa’id KhatibZadeh ne ya yi kira ga kasashen da suke yaki da Yemen da su daukewa wannan kasar takunkumin da su ka kakaba ma ta, domin sun fahimci kuskuren da su ka tafka a tsawon shekaru 6.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran wanda yake yin tsokaci akan furucin da jami’an gwamnatin Amurka su ke yi akan yakin kasar Yemen, ya ci gaba da cewa; Idan dai har dakatar da sayar makamai ga Saudiyya ba wasa ba ne na siyasa, to zai iya zama abinda da ya dace domin warware kurakuren baya.
KhatibZadeh
ya kuma ce; Wannan matakin kadai ba zai iya warware matsalar kasar Yemen ba, da
akwai bukatar a kawo karshen killace kasar da aka yi ta sama, ruwa da kasa wanda ya yi sanadin
mutuwar dubban mutane saboda rashin abinci mai gina jiki.
Wani sashe
na bayanin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya kunshi dorawa
kungiyoyin kasa da kasa alhakin laifukan da Saudiyya ta tafka a kasar Yemen.
031
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!