​Najeriya: Hukumar Zabe Za Ta Kara Yawan Mazabu Kafin Zaben Shekara Ta 2023

2021-02-06 19:03:57
​Najeriya: Hukumar Zabe Za Ta Kara Yawan Mazabu Kafin Zaben Shekara Ta 2023

Hukumar Zaben Najeriya INEC ta bayyana cewa ta fara shirye-shiryen samar da karin mazabu a fadin kasar kafin zaben 2023.

A cikin rahoton da jaridar Premum Times ta bayar ta bayyana cewa, shugaban kwamitin wayar da kan masu zabe Festus Okoye ya bayyana cewa, suna da shirin kara yawan mazabun ne a dukkanin sassan Najeriya.

Okoye ya kara da cewa, a watan Agustan 2014 hukumar zaben Najeriya ta gabatar da bukatar samar da karin mazabu 30, 027, inda yankin arewacin kasar zai samu karin muzabu 21,615 yayin da yankin kudancin kasar kuma zai samu 8,412.

Sai dai wannan bukatar da hukumar zaben ta gabatar, ta jawo sabani a tsakanin bangarorin ‘yan siyasa, wanda hakan yasa aka dakatar da batun, duk kuwa da cewa shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa, a halin yanzu Najeriya ba ta da isassun mazabu a fadin kasar.

Tun kafin wannan lokacin ana yin korafi kan yadda ake samun matsaloli a wasu yankuna a yayin gudanar da zabuka a kasar, inda wasu yankunan kan gudanar da zabuka a karkashin mazabu da ke cikin wasu yankunan na daban.

Wannan yana faruwa ne a cewar hukumar zaben, saboda kasantuwar mazabun da ke akwai a Najeriya ba su wadatar ba, wanda kuma hakan shi ne babban dalilin da yasa aka gabatar da shawarar kara yawan mazabun a fadin kasar.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!