Amurka: Majalisar Dattijai Ta Dakatar Da Marjorie Taylor Daga Wasu Kwamitocin Majalisar

An kori ‘yar majalisar dattijan Amurka mai tsananin kiyayya
da addinin musulunci Marjorie Taylor Green daga wasu kwamitocin majalisar.
Kafofin yada labaran Amurka sun
bayar da rahoton cewa, majalisar dattijan Amurka ta kori ‘yar majalisa mai
tsananin kiyayya da addinin musulunci Marjorie Taylor Green daga wasu
kwamitocin majalisar sakamakon yadda take ta kawo matsaloli da haifar da rashin
jituwa a tsakanin ‘yan majalisar.
Wannan 'yar majalisa wadda ta ci
zabe 'yan watannin da suka gabata wanda ya ba ta damar zama 'yar majalisar
dattijan Amurka, a cikin 'yan makonnin nan tana furta maganganu na neman tayar
da zaune tsaye a cikin majalisar.
Daga cikin irin maganganun da take
yi kuwa har da ikirarin cewa Donald Trump ne ya ci zabe, an dai murde masa ne
kawai aka dora Joe Biden, kamar yadda kuma take nuna goyon bayanta ga tunzura
magoya bayansa da Donald Trump ya yi suka kaddamar da farmaki kan majalisa.
Wannan yasa ta samu sabani hatta da
su kansu 'yan majalisar dattijan da suka fito daga jam'iyyarta ta Republican,
inda da dama daga cikinsu suka mara baya ga shawarar da aka gabatar kan korarta
daga cikin kwamitocin majalisar guda biyu da aka sanya ta a matsayin mamba.
Wannan 'yar majalisar dattijan
Amurka da ke wakiltar jihar Georgia, ta yi kaurin suna wajen kin addinin
musulunci da musulmi, musamman a lokacin mulkin Trump inda masu irin wannan
ra'ayi suke samun goyon baya da kariya kai tsaye daga gwamnati.
015