Janar Hatami: Gwajin Rokar Dakon Tauraron Dan Adam Da Iran Ta Yi, Ci Gaba Ne Na Ilimi

2021-02-06 14:42:40
Janar Hatami: Gwajin Rokar Dakon Tauraron Dan Adam Da Iran Ta Yi, Ci Gaba Ne Na Ilimi

Ministan Tsaron Iran Ya Ce, Kera Makami Mai Linzami Na “Zul-Jihan” Na Dakon Tauraron Dan Adam Da Kasar Ta Yi Ya Sake Tabbatar Da Ci Gabanta Ne Na ilimi.

Ministan tsaron na Iran Birgediya Janar Amir Hatami wanda yake ziyarar aiki a kasar India ya gana da daliban Iran da suke karatu a can, yana mai cewa; Samarin Iran sun tabbatar da kwazonsu a fagage daban-daban na Iran.

Birgediya janar Amir Hatami ya kuma ce; Makami mai linzamin mai sunan; Zul-Jinah’ na daukar tauraron dan’adam dalili ne akan ci gaban ilimi da Iran din take samu.

Wani sashe na jawabin ministan tsaron na Iran ya bayyana cewa; Juyin juya halin musulunci a karkashin jagorancin Imam Khumaini ( R.A) ya cusawa al’ummar Iran dogaro da kansu, da jin cewa za su iya kutsawa cikin duk wani fage na ci gaba.

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!