Ghana Za Ta Karbi Rigakafin Covid-19 A Watan Fabrairu

2021-02-06 14:38:40
Ghana Za Ta Karbi Rigakafin Covid-19 A Watan Fabrairu

Maganin da Ghana za ta karba na AstraZeneca da jami’ar Oxford ta samar ne, adadinsa kuma zai kai miliyan 2.4 kamar yadda aka sanar a kasar.

Hr ila yau, shirin samarwa da kasar ta Ghana yana a karkashin hukumar lafiya ta kasa da kasa ne, ( WHO), kuma ya hada da wasu kasashen da su ka kai 144.

Ya zuwa yanzu dai adadin wadanda su ka kamu da cutar tun bullarta sun kai 70,046, yayin da wadanda su ka warke kuma sun kai 63,503.

Wadanda kuma su ka rasa rayukansu sanadiyyar cutar sun kai 446.

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!