Iran Za Ta Karbi Riga Kafin Cutar Korona Na Kamfanin Astra Zeneca

2021-02-06 09:58:48
Iran Za Ta Karbi Riga Kafin Cutar Korona Na Kamfanin Astra Zeneca

Jakadan kasar Iran a birnin London na kasar Burtaniya ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba alluran riga kafin cutar koron samfurin Astra Zeneca zai isa kasar Iran nan ba da dadewa ba.

Majiyar muryar Jamhuriyar musulinci ta Iran ta nakalto Muhammad Sa’idi-Najad yana fadar haka ne a jiya jumma’a shafins ana twitter. Ya kuma akara da cewa tuni alluran riga kafin cutar ta korona mai suna Sputnik na kasar Rasha ta isa kasar, kuma za’a fara yiwa jami’an kiwon lafaya alluran da farko don karesu daga kamuwa da cutar.

Jakadan kasar Iran a London ya klara da cewa ya zuwa yanzu an yi mutani kimani miliyon 10 alluran riga kafin a duniya amma duk da haka ana ci gaba da samun wadanda suke kamuwa da cutar a kasashen turai da Amurka . wannan ya nuna an abukatar yiwa mutanen da dama alluran kafin a fara ganin addainin masu kamuwa su fara ragiwa a ko wacce yini.
Tags: astra zeneca
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!