Amurka Ta Amince Okonjo-Iweala Ta Shugabanci Kungiyar WTO
2021-02-06 09:47:06

Gwamnatin kasar Amurka ta amincea da Dr Ngozi Okonjo-Iweala a
matsayin shugaban kungiyar kasuwanci ta duniya, wato World Trade Organisation.
Ko WTO.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa gwamnatin shugaba
Biden ta dauki wannan matakin ne bayan da gwamnatin kasar Korea ta Kudu ta bada
sanarwan janye dan takaranta na neman wannan mukamin.
Harila yau Larabarin ya kara da cewa Okonjo –Iweala tana da
korewa a cikin ayyukan harkar kaswanci da banki na tsawon shekaru 25 sannan ta
rike mukamin ministan kudi a Najeriya na tsawon shekaru biyu wadanda suka bada
damar neman wannan matsayin.
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!