Iraki:Daesh Ta Kai Hari Kan Cibiyar ‘Yansanda A Lardin Kirkuk

Ragowar mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a kasar Iraki
sun kai hari kan wata cibiyar ‘yan sandan gwamnatin kasar dake a birnin Kirkuk.
Kamfanin dillancin labaran ‘Sabirun News’ na kasar ta Iraki wanda
yake karkashin jami’an tsaron kasar ya bada sanarwan cewa ragowar mayakan Daesh
a kasar sun kai hari kan wata cibiyar ‘yansandan a daren jiya Jumma’a, sai dai labarin bai bayyana yawan asarori na
rayuka da dukiyoyin da aka yi ba, har zuwa lokacin bada wannan labarin.
Tun shekara ta 2017 ne jami’an tsaron gwamnatin kasar ta Iraki,
wadanda suka hada da hashdushabi suka sami nasara kawo karshen ikon kungiyar a
wasu yankunan kasar Iraki da ta mamaye, amma har yanzun akwai ragowarsu wadanda
suke kaiwa jami’an tsaron kasar hare-hare nan da can.
Lardunan da abin ya fi shafa dai a halin yanzu suna hada da
Diyala, Kirkuk, Ninawa, Salahuddeen, Ambar da kuma Bagdaza babban birnin kasar.