Sojojin Siriya Sun Kakkaɓo Makamai Masu Linzami Da Isra’ila Ta Harbo Cikin Ƙasar

Makaman kare sararin samaniya na sojojin ƙasar Siriya sun kakkaɓo wasu makamai masu linzami na haramtacciyar ƙasar Isra’ila da aka harbo su cikin ƙasar daga ta ɓangaren yankin Tuddan Golan da Isra’ilan ta mamaye.
Kamfanin
dillancin labaran ƙasar Siriyan ne ya bayyana hakan a yau ɗin nan inda ya ce da
misalin ƙarfe 10:42 na daren jiya Laraba, sojojin Isra’ila sun kawo hari ƙasar
Siriyan daga yankunan Tuddan Golan inda suka harbo wasu makamai masu linzami da
ake harbo su daga sama zuwa ƙasa da kuma waɗanda ake harbo su daga ƙasa zuwa
ƙasa a wani yanki da ke Kudancin ƙasar ta Siriya.
Kamfanin
dillancin labaran ya ci gaba da cewa sai dai dakarun Siriyan sun sami nasarar
kakkaɓo waɗannan makamai a yankin Kudu masu yammacin lardin Quneitra da ke
Siriyan.
Gidan
talabijin ɗin ƙasar Siriya ya nuna wani ɓangaren na kakkaɓo makaman da dakarun
Siriyan suka yi.
Wasu
majiyoyin sojin Siriyan sun ce an sami nasarar kakkabo mafi yawa daga cikin
makaman da aka harbo din duk da cewa wasu sun sauka a wasu wajajen waɗanda ba
su yi wata ɓarna ta a zo a gani ba.
Sojojin Isra’ilan dai suna yawan kawo irin waɗannan hare-hare kan dakarun Siriyan da ma na Hizbullah da suke taya su faɗa duk kuwa da cewa hakan bai hana sojojin Siriyan ci gaba da samun nasararori a kan ‘yan ta’addan da Isra’ilan da Amurka suke goya wa baya a Siriyan ba.