​Iran Da Iraki Sun Cimma Matsaya Kan Kara Fadada Alakarsu A Dukkanin Bangarori

2021-02-04 15:06:55
​Iran Da Iraki Sun Cimma Matsaya Kan Kara Fadada Alakarsu A Dukkanin Bangarori

Gwamnatocin kasashen Iran da Iraki sun cimma matsaya kan kara bunkasa alaka a tsakaninsu a dukkanin bangarori.

A cimma hakan ne a ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Iraki Fu’ad Hussain ya gudanar ne a kasar ta Iran, inda ya gana da manyan jami’an gwamnatin kasar kan batutuwa da daban-daban da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma yadda za a kara bunkasa ta.

Fu’ad Hussain ya gana da takwaransa na kasar Iran Muhammad Jawad Zarif, kamar yadda kuma ya gana da shugaba Hassan Rauhani, gami da shugaban majalisar dokokin kasar ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf da kuma babban sakataren majalisar tsaron kasa Admiral Ali Shamkhani.

Bangarorin biyu dai sun cimma matsaya kan ci gaba da yin aiki tare tsakanin gwamnatocin Iran da Iraki, a bangarori na siyasa, tsaro da kuma bunkasa harkokin tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu, inda aka rattaba hannu a kan yarjeniyoyi daban-daban a yayin ziyarar a wadannan fagage.

Kasar Iran ce babbar makwabciya ga kasar Iraki, inda al’ummar Iraki sukan samu mafi yawan kayayyakin da suke bukata na harkokin yau da kullum daga kasar ta Iran, kamar yadda kuma yankuna da dama a cikin kasar Iraki, suna samun wutar lantarki ne kai tsaye daga kasar ta Iran.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!