​Isra’ila Na Ci Gaba Da Tona Manyan Ramuka A Karkashin Masallacin Aqsa

2021-02-04 15:03:38
​Isra’ila Na Ci Gaba Da Tona Manyan Ramuka A Karkashin Masallacin Aqsa

Gwamnatin Isra’ila na ci gaba da gudanar da aikin tonon ramuka a karkashin masallacin Aqsa mai alfarma.

Rahotanni daga Palestine na cewa, yahudawan Isra’ila suna ci gaba da aikin tonon manyan ramuka a karkashin masallacin aqsa, da nufin rusa katangar nudba da ke masallacin, inda suke nufin yin wani gini na daban domin shafe daya daga cikin manyan alamu na muslunci da ke a wannan masallaci mai alfarma.

Masani kan harkokin siyasar Isra’ila Abu Diyab ya bayyana cewa, tun kafin wannan lokacin yahudawan suka fara wannan aiki, wanda kungiyoyin farar hula na duniya gami da gwamnatocin kasashe daban-daban da suka hada har da na turai, duk sun yi Allawadai da hakan.

Ya ci gaba da cewa, yahudawan suna da nufin gina wani wuri ne da zai ba su damar samar da wurin ibadar yahudawa a cikin masallacin, amma suna son gina wurin ne ya zama mai hawa uku, ta yadda za su rarraba shi zuwa wurin bauta da kuma wurin horar da malaman yahudawa da wuraren karatu da sauransu.

A nasa bangaren Najeh Bukairat, mataimakin babban sakataren cibiyar da ke kula da harkokin musulunci a birnin Quds ya bayyana cewa, yahudawan sun yi amfani da wanann lokaci na corona wajen hana musulmi yin salla a cikin masallacin Quds, wanda hakan ya ba su damar yin aikin rusa wasu bangarorin masallacin hankali kwance.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!