Nijar : Jam’iyyu Na Kafa Kawance Domin Fafatawa A Zagaye Na Biyu

2021-02-04 09:54:29
Nijar : Jam’iyyu Na Kafa Kawance Domin Fafatawa A Zagaye Na Biyu

A Jamhuriyar Nijar, jam’iyyar MNDS-Nassara da kuma MPR-Jamhuriya, wadanda su ne suka zo na uku da kuma na hudu a zaben shugabancin kasar zagaye na farko sun goyi bayan dan takaran jam’iyya mai mulki ta PNDS-tarraya.

A sanarwowin da suka fitar a jiya Laraba, jam’iyyun sn bukaci magoya bayan su dasu kada kuri’a gad an takarar jam’iyyar mai mulki cewa da Malam Bazoum Mohamed.

A ranar 21 ga watan Fabrairun nan ne za’a fafata a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu, tsakannin Bazoum Mohamed na jam’iyyar PNDS tarayya da kuma tsohon shugaban kasar Alhaji Mahamane Usman karkashin jam’iyyar RDR-Chanji, dake samun goyan bayan jagoran ‘yan adawa na kasar Malam Hama Amadu.

Ita mai dai jam’iyyar ta RDR, ta samu goyan baya a kwanakin baya daga wasu jam’iyyun siyasar da suka hada da UDFP SAWABA da FRC, da kuma PJP-DUBARA, ta tsohon shugaban mulkin soja Janar Saluhu Djibo, da wasu jam’iyyu dakae masa kawance.

A ranar 30 ga watan Janairu da ya gabata ne Kotun tsarin mulki a Jamhuriyar Nijar, ta fitar da sakamakon dindindin na zaben shugaban kasar zagayen farko da aka gudanar a ranar 27 ga watan Disamba da ya gataba.

Sakamakon da kotun tsarin mulkin kasar ta fitar a cikin daren jiya Asabar, ya nuna dan takara M. Bazoum ne kan gaba da kashi 39,30 cikin dari, sai kuma M. Mahamane Usmane, dake biye masa da kashi 16,98 cikin dari na yawan kuri’un da aka kada, wanda hakan ya tabbatar da sakamakon wucin gadi da hukumar zaben kasar ta CENI ta fitar a ranar 2 ga watan Janairun nan.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!