MDD Ta Yi Maraba Da Kara Wa’adin Takaita Makaman Nukiliya

2021-02-04 09:50:13
MDD Ta Yi Maraba Da Kara Wa’adin Takaita Makaman Nukiliya

MDD ta bayyana a jiya Laraba cewa, ta yi maraba da matakin kasashen Amurka da Rasha, na kara wa’adin yarjejeniyar takaita mallakar makaman nukiliya mai lakabin ‘’sabuwar tafiya’’ wato (NewSTART) zuwa shekaru biyar.

Da yake karin haske kan batun yayin taron manema labarai, mai magana da yawun babban sakataren MDD Antonio Guterres, Stephan Dujarric, ya bayyana cewa, majalisar ta yi matukar farin ciki da karin wa’adin, wanda ta ce wani mataki ne na takaitawa manyan kasashen duniya mallakar makaman nukiliya. Kuma matakin farko ne da zai karfafa takaita mallakar makaman.

Ya ce, a nata bangaren, majalisar tana karfafawa kasashen Amurka da Rasha gwiwa, da su yi amfani da shekaru biyar din dake tafe, wajen kara tattauna yadda za su rage makaman nukiliyar da suka mallaka, da kulla sabbin yarjeniyoyi da za su magance sabbin kalubalen makamai da muke fuskanta a wannan zamani.

Kakakin ya kuma bayyana fatan cewa, karin kasashe da suka mallaki makaman nukiliya, za su bi sahun kokarin da ake na kwance damarar makaman nukiliya.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!