Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa Ta Real Madrid Ya Kamu Da Cutar Korona

2021-02-03 22:28:43
Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa Ta Real Madrid Ya Kamu Da Cutar Korona

Jaradira Premuim times ta Najeriya ta nakalto majiyar kungiyar Reala Madrid ta na cewa shugaban kungiyar ya kamu da cutar korona.Jaridar ta kara da cewa, Florentino Perez, dan shekara 73 a duniya ya kamu da cutar ne a gwaji na karshe da aka yi masa, kuma tuni ya killace kansa don jinyar cutar.

Labarin ya kara da cewa Perez bai da alamun cutar a zahiri, amma ana masa gwajin cuyar a a kai a kai, wanda ya sa alamun kamuwa da cutar suka bayyana a gwajin da aka yi masa na karshe karshen nan.

Kungiyar Real Madrid ta kammala da cewa wannan labarin ya na zuwa ne a dai dai ranar da kocin kungiyar Zinedine Zidane yake dawowa bakin aiki, bayan jinyar cutar ta korona wacce ya kamu da ita a ranar 19 ga watan Jenerun da ya gabata.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!