Allah Ya yi wa Farfesa Dahiru Yahaya Rasuwa, Sakamakon Rashin Lafiya

2021-02-03 17:08:08
Allah Ya yi wa Farfesa Dahiru Yahaya Rasuwa, Sakamakon Rashin Lafiya

Rahotanni daga birnin Kano, Nijeriya sun bayyana cewar Allah Ya yi wa sahararren masani kana malamin jami’a, Farfesa Dahiru Yahaya rasuwa yana da shekaru 75 a duniya bayan rashin lafiya da yayi fama da shi.

Rahotannin sun ce Farfesa Dahiru Yahaya wanda ya kasance tsohon malami ne da yayi koyarwa a jami’oin Bayero da ke Kano (BUK) da kuma Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya ya rasu ne a yau din nan Laraba a wani asibiti a Kanon bayan dan gajeren rashin lafiya.


Wasu kafafen watsa labarai sun jiyo daya daga cikin ‘yan’uwan marigayi Farfesa Dahiru Yahayan, wato Bashir Habib Yahaya yana cewa a yammacin yau din ne dai za a yi wa marigayi salla da kuma bisne shi kamar yadda dokokin addinin Musulunci suka tanada a gidansa da ke Ungogo da ke Kanon.


Malam Bashir ya kara da cewa marigayin ya rasu yana da shekaru 75 a duniya kuma ya rasu ya bar mata uku, ‘ya’ya ashirin da biyu da kuma jikoki da dama.


Baya ga koyarwa a jami’oi har ila yau kuma Farfesa Yahaya yayi rubuce-rubuce kan batutuwa daban-daban bugu da kari kan lakcoci daban-daban da ya dinga gabatarwa.

Daga cikin lakcocinsa da suka dau hankula har da wadanda ya gabatar a lokuta mabambanta a Husainiyar Baqiyatullah ta harkar Musulunci a Nijeriya karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Yakub El-Zakzaky haka nan kuma da shaidar da ya bayar a wajen kwamitin binciken da aka kafa don binciko abin da ya faru a Zariya a shekara ta 2015 bayan harin da sojoji suka kai wa 'yan harkar Musuluncin.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!