Tarayyar Turai Tana Tattaunawa Da Amurka Domin Dauke Wa Iran Takunkumi

Majiyoyin kungiyar tarayyar turai
sun ce jami’an kungiyar suna tattaunawa da Amurka domin dauke wa Iran
takunkuman da ta kakaba mata.
Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton
cewa, wani bayani da ta samu daga ofishin babban jami’i mai kula da harkokin
siyasar wajen kungiyar tarayyar, na tabbatar da cewa jami’an kungiyar suna
tattaunawa da Amurka domin dauke wa Iran takunkumai.
Rahoton ya ce kungiyar tarayyar
turai na kokarin ganin Amurka ta dawo cikin yarjejeniyar nukiliya da aka
cimmawa tare da Iran a 2015, yarjejeniyar da tsohon shugaban kasar Amurka
Donald Trump ya fitar da kasar ta Amurka a cikin shekara ta 2018, tare da sake
mayar wa Iran din da takunkuman da aka dauke mata.
Tun lokacin yakin neman zabe, sabon
shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi ta nata cewa, idan ya lashe zabe zai
mayar da Amurka cikin wanan yarjejeniya, matukar dai Iran ta ci gaba da yin
aiki da ita.
Bayan ficewar Amurka daga
yarjejeniyar, da kuma kasa aiwatar da wasu alkawulla da kasashen kungiyar
tarayyar turai suka dauka, Iran ta jingine yin aiki da wasu bangarorin
yarjejeniyar, tare da bayyana cewa za ta ci gaba da yin aiki da su bisa
sharadin cika mata alkawullan da kasashen turai suka dauka.
A halin yanzu dai Iran ta ci gaba da
shirinta na tace kashi 20% na sanadarin uranium, wanda kasashen turan ke fargabar
cewa Iran za ta iya kera makaman nukiliya da shi.
015