Rasha Ta Kirayi Kasashen Turai Da Su Guji Tsoma Baki A Harkokinta Na Cikin Gida Kan Batun Navalny

Ma’aikatar harkokin wajen kasar
Rasha ta kirayi kasashen turai da su guji tsoma bakinsu a cikin harkokin Rasha na
cikin gida, dangane da batun shari’ar Alexey Navalny.
Mai magana da yawun ma’aikatar
harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova c eta bayyana hakan a zanyawarta da
tashar RBK ta kasar Rasha, inda ta bayyana cewa, batun Navalny magana ce ta
cikin gida da ta shafi Rasha, ba shi da wata alaka da kasashen turai.
Ta ci gaba da cewa, har kullum abin
da yake da muhimmanci shi ne kasashe su mayar da hankulansu ga abin da ya shafe
su, musamman kasashen turai da suke da matsaloli da dama na cikin gida, wanda
ya kamata su mayar da hankali kansu, maimakon sanya ido a kan Rasha da
harkokinta na cikin gida.
Kotun kasar Rasha ta yanke hukuncin
daurin shekaru 3 da rabi a gidan kaso, bayan samunsa da laifuka da suka
danganci yaudara, da kuma saba wa dokar daurin talala, da hakan ya hada da
fitar da ya yi daga kasar ba bisa ka’ida ba.
A bisa wannan hukunci dai zai yi
kimanin shekaru biyu da rabi ne gidan kaso, bisa la’akari da cewa ya yi shekara
guda ana yi masa daurin talala kafin wannan lokaci, amma lauyoyinsa sun ce za
su daukaka kara a cikin kwanaki 10 masu zuwa, wanda shi ne wa’adin da suke da
shi kafin hukunci ya fara aiki.
015