Iran Ta Mayar Da Martani Ga Kalaman Shugaban Faransa Kan Shigo Da Saudiyya Cikin Yarjejeniyar Nukiliya

2021-02-02 20:08:35
Iran Ta Mayar Da Martani Ga Kalaman Shugaban Faransa Kan Shigo Da Saudiyya Cikin Yarjejeniyar Nukiliya

Mai magana da yawun gwamnatin Iran, Ali Rubai’iy, ya mayar da martani ga kalaman shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, na wajibcin shigo da Saudiyya cikin yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da Iran yana mai bayyana kalamin a matsayin wani kalami na rashin mafaɗi.

Mai magana da yawun gwamnatin ta Iran ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a yau ɗin nan Talata inda ya ce a lokuta da dama kana kuma a fili Iran ta sha bayyana cewar ba za ta amince da gudanar da wata sabuwar tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliya ba, don haka babu ma wata magana ta shigo da wasu ƙasashe na daban cikinta.

Mr. Rubai’iy ya ƙara da cewa: A saboda babu wata hanya da ta rage face dai Amurka ta dawo cikin yarjejeniyar sannan sauran ƙasashen da suke cikinta, ciki kuwa har da ƙasar Faransan, kuma su aiwatar da nauyin da ke wuyansu.

Kakakin gwamnatin ta Iran ya bayyana cewa kalaman shugaban ƙasar Faransa na cewa wajibi ne a shigo da Saudiyya cikin yarjejeniyar a matsayin wani kalami na rashin mafaɗi wanda Iran ba za ta taba amincewa da shi ba.

Yayin da kuma yake magana dangane da kiran da Amurka ta yi na cewa wajibi ne Iran ta dawo cikin yarjejeniyar gaba ɗaya kafin ita ma ta dawo ciki, Kakakin gwamnatin na Iran ya ce Amurka ita ce ƙasa guda ɗaya tilo da ta fice daga yarjejeniyar don haka ita ce ya wajaba a gare ta ta dawo ciki.

A kwanakin baya ne dai shugaba Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewar akwai buƙatar a shigo da Saudiyya cikin yarjejeniyar nukiliyan lamarin da ake ganinsa a matsayin abin da ke tabbatar da raɗe-raɗin da ake yi na cewa Saudiyya ta ba wa Macron ɗin kwangilar ƙoƙarin tabbatar mata da muradinta a ƙasashen duniya sakamakon kawo ƙarshen gwamnatin tsohon shugaban Amurka Donald Trump wanda ke biya mata wannan buƙata.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!