‘Yan Gwagwarmayar Falastinawa Sun Harbo Wani Jirgin Isra’ila Mara Matuƙi A Gaza

2021-02-02 20:03:20
‘Yan Gwagwarmayar Falastinawa Sun Harbo Wani Jirgin Isra’ila Mara Matuƙi A Gaza

Rahotanni daga Zirin Gaza sun ce dakarun gwagwarmayar Falastinawa sun harbo wani jirgin sama mara matuƙi na sojojin haramtacciyar ƙasar Isra’ila a Kudancin Zirin na Gaza a yau ɗin nan.

Majiyoyin labarai daga Gazan sun ce a safiyar yau ne dai dakarun gwagwarmayar suka harbo jirgin a gabashin garin Khan Yunis bayan da suka sami damar kwace ikon tafiyar da jirgin.

Rundunar sojin Isra’ilan ma dai ta sanar da cewa ɗaya daga cikin jiragenta marasa matuƙa ya faɗo a Gaza yayin wani aiki da yake yi a can, sai dai ta yi ikirarin cewa ‘babu wani haɗari na yiyuwar bayyanar wasu bayanan sirri.

Wannan dai shi ne karo na uku da ake harbo jiragen sojojin ‘Isra’ila’ marasa matuƙa cikin wannan makon a Zirin Gazan da kuma Kudancin Labanon.

A ranar Lahadin da ta gabata, dakarun Falastinawa sun harbo wani jirgin Isra’ilan da ke ayyukan leƙen asiri a sararin samaniyyar Beit Hanoun da ke arewacin Gazan. Washegari kuma dakarun ƙungiyar Hizbullah na ƙasar Labanon su ma sun harbo wani jirgin saman Isra’ilan mara matuƙi lokacin da ya shigo sararin samaniyyar ƙasar a kusa da ƙauyen Blida.

Harbo waɗannan jiragen leƙen asirin da dakarun gwagwarmayar suke yi a Gaza da kuma Labanon yana nuni ne da irin ƙarfin da dakarun suke ƙara yi ne a ci gaba da gwagwarmaya da kuma faɗar da suke yi da yahudawa ‘yan mamayan.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!