Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Fara Aiwatar Da Sabon Tsarin Ritaya Na Malaman Makarantu

2021-02-02 20:01:06
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Fara Aiwatar Da Sabon Tsarin Ritaya Na Malaman Makarantu

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da cewa tuni aka fara aiwatar da sabon tsarin shekarun ritaya da aiki na malaman makarantu a ƙasar wanda a kwanakin baya gwamnatin ta amince da shi.

Babban sakatare a ma’aikatar ilimi ta tarayya ta Nijeriyan, Sonny Echono ne ya sanar da hakan, cikin wata sanarwa ga manema labarai da ya fitar a Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriyan inda ya ce tun daga ranar 1 ga watan Janairun da ya gabata aka fara aiwatar da wannan tsarin.

A kwanakin baya ne dai gwamnatin Tarayyar Nijeriyan bayan zaman da majalisar zartarwa ta ƙasar ta gudanar ta sanar da cewa an amince da shekaru 65 a matsayin shekarun ritaya da kuma shekaru 40 a matsayin shekarun aiki ga malamai a duk faɗin ƙasar.

Kafin hakan dai shekaru 60 shi ne shekarun ritayar malaman sannan shekarun da za a yi ana aikin shi ne shekaru 35.

Sai dai Mr. Echono ya ce wajibi ne malaman sun tabbatar da suna da cikakken lafiya kafin wannan sabon tsarin ya fara aiki a kansu yana mai cewa za a buƙaci malaman da su gudanar da gwajin lafiya tukun, wanda aka same shi da ba shi da cikakken lafiya to za a buƙaci da yayi ritaya.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!