‘Yan Gudun Hijirar Rohingya Sun Yi Kira Da Kada A Tausaya Wa Suu Kyi

A daidai lokacin da ake ta mayar da martani mabambanta dangane da juyin mulkin sojin da aka yi a ƙasar Myammar, ‘yan gudun hijiran Rohingya na ƙasar da suke gudun hijira a ƙasar Bangladesh sun yi Allah wadai da juyin mulkin sojin sai dai sun ce ba su tausaya wa shugabar ƙasar Aung San Suu Kyi saboda kifar da ita da aka yi ba.
A wata hira da yayi da
tashar talabijin ta Aljazeera, shugaban ‘yan gudun hijiran na Rohingya Mohammad
Yunus Arman ya ce ba su tausaya wa Aung San Suu Kyi ɗin ko kaɗan ba don kuwa
lokacin da sojojin suke kashe al’ummar Rohingya a jihar Rakhine tana kan mulki
kuma ba ta ce komai ba.
Mr. Arman ya ci gaba da
cewa: A baya mun kasance muna mata addu’a don ta sami nasara kuma muna ɗaukarta
tamkar wata sarauniya, to amma bayan shekara ta 2017 mun fahimci haƙiƙanin
halayenta.
Don haka ya ce a halin
yanzu kan ba ma tausaya mata don an kifar da ita daga mulki.
Sama da ‘yan gudun
hijiran ƙasar Myammar ɗin miliyan guda mafi yawansu musulmi ‘yan Rohingya ne
waɗanda suka gudu suka bar ƙasar sakamakon kisan kiyashin da sojoji da mabiya
addinin Buddha masu tsaurin ra’ayi suke musu ba tare da gwamnatin Aung San Suu
Kyi ɗin ta hana su ba.
A jiya Litinin ne dai sojojin ƙasar Myammar ɗin suka yi wa gwamnatin ƙasar ta Aung San Suu Kyi juyin mulki inda suke ci gaba da tsare ta.