​Zarif: Amurka Ta Daina Cinikin Makamai A Gabas Ta Tsakiya Kafin Ta Yi Magana Kan Makaman Iran

2021-02-02 14:01:15
​Zarif: Amurka Ta Daina Cinikin Makamai A Gabas Ta Tsakiya Kafin Ta Yi Magana Kan Makaman Iran

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, ya kamata ne Amurka ta daina sayar da makamai na daruruwan biliyoyin daloli a yankin gabas ta tsakiya, kafin ta yi magana a kan makamai masu linzami na Iran.

A wata zantawa da ya yi da tashar CNN a daren jiya, Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, batun kafa wasu sharudda a kan yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tsakanin Iran da manyan kasashen duniya bai taso ba, domin kuwa yarjejeniya tana nan a rubuce, abin ya rage shi ne a yi aiki da ita.

Zarif bijiro da batun saka wani abu daban da ba shi da alaka da batun shirin nukiliya na Iran, hakan ba shi da wata ma’ana, a kan hakan gwamnatin Joe Biden ta sake yin nazari kan tunanin da take yi a kan wannan batu.

Ya ci gaba da cewa, yanzu haka dukkanin makaman da ake yin amfani da su wajen kisan jama’a a gabas ta tsakiya kasashen turai ne musamman Amurka ta sayar da su ga gwamnatoci ‘yan ina da yaki a gabas ta tsakiya, kuma duniya tana ganin yadda ake yin amfani da wadannan makamai wajen kisan mata da kananan yara a kasar Yemen.

Daga karshe ya jaddada cewa, Iran ba za ta ja da baya ba kan matsayar da ta dauka, kuma ya rage ga sauran bangarorin yarjejeniyar da su yi nazari kan hakan, matukar dai suna bukatar wanzuwar wannan yarjejeniya a raye.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!